fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Da Dumi Dumi: ‘Yan majalisa tara na PDP sun koma jam’iyyar ANPP a jihar Kano

Jam’iyyar PDP ta rasa membobinta na majalisa guda tara a jihar Kano inda suka koma sabuwar jam’iyyar ANPP.

A kwanakin baya shugaban PDP na jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya koma jam’iyyar ANPP, kuma yanzu mai magana da yawun ‘yan majalisar Uba Abdullahi ya tabbatar da cewa mutane tara sun sake koma ANPP.

Yace sun aiko da wasika cewa ba zasu iya tafiyar PDP bane domin akwai matsaloli a jam’iyyar kama daga sama har izuwa kan jihohi, sobada haka ne suka sauya sheka.

Kuma ga sunayen au kamar haka. Isyaku Ali Danja (Dan majalisar Gezawa ), Umar Musa Gama (Dan majalisar Nassarawa), Aminu Sa’adu Ungogo (Dan majalisar Ungogo), Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa (Dan majalisar Dala) da Tukur Muhammad (Dan majalisar Fagge).

Karanta wannan  Hotuna:Osinbajo ya kai ziyara Kano inda Tukunyar gas ta fashe

Sai kuma Mu’azzam El-Yakub (Dan Majalisar Dawakin Kudu), Garba Shehu Fammar (Dan majalisar Kibiya), Abubakar Uba Galadima (Dan manalisar Bebej) da Mudassir Ibrahim Zawaciki (Dan majalisae Kumbotso).

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.