Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan bangar siyasa ne sun kaiwa jirgin kasan yakin neman zaben gwamnan Osun hari watau, Adegboyega Oyetola.
‘Yan ta’addan sun kai harin ne a ranar litinin kuma a ciki hadda motar manema labarai ta NUJ wadda itama suka lalata ta.
Kuma sun jiwa wasu manema labarai rauni. A takaice dai sun lalata motoci kusan goma a harin da suka kaiwa gwamnan.