A safiyar yau ne aka samu labari ‘yan ta’addan Boko Haram sun kaiwa jami’an yan sanda hari a kauyen Goni Matari dake jihar Borno.
Inda suka kashe jami’ai biyu kuma suka jiwa biyar rauni, kuma suka kona masu motoci biyu kamar yada DailyTrust suka ruwaito.
Yan ta’addan Boko Haram din sun tsere bayan da suka ga wata rundunar ‘yan sandan ta kawo masu dauki.