fbpx
Monday, August 8
Shadow

Da Dumi-Dumi:An samu wanda ya Mutu Sanadin Coronavirus/COVID-19 a legas

Rahotanni daga Jihar Legas na cewa wani mutum me shekaru 55 ya mutu a Asibiti  koyarwa na jami’ar Legas din.

 

Wata majiya daga Asibitin, ta shaidawa jaridar Punch cewa, bayan mutuwar mutumin an wa gawarshi gwajin cutar Coronavirus kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa yana dauke da cutar.

 

Majiyar ta kara da cewa mutumin na da cutar hawan jini data suga da kuma Ciwon koda me tsanani.

 

Majiyar ta bayyana cewa Mutumin bai bayyana cewa ko ya fita zuwa kasar waje a ‘yan kwanakinnan ba ko kuma yayi mua’alama da wani daya fita kasar waje ba.

 

Mutumin ya je Asibitinne da daren Alhamis kuma bai da matsalar tari ko ciwon gabbai ko na zawo ba

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.