Shugaba Muhammadu Buhari yayi tsokaci akan kashe kashen da yan bindiga keyi a karamar hukumar Kanam da Watse dake jihar Plateau.
Inda yace abin yayi muni kuma gwamnati ba zata taba raga masu ba tare da masu daukar nauyin su, kuma ya sha alwashin kawo zaman lafiya a jihar dama Najeriya bakidaya.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan ranar talata, kuma a karshe yace gwamnati ba zata taba yafewa masu aikata wannan laifin ba.