fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Da Dumi-Dumi:Bidiyon yanda Sojojin Najeriya suka kashe wasu manyan shuwagabannin Boko Haram

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa sojojin sama sun kai wani hari a yankin Garin Maloma dake dajin Sambisa inda suka kashe wasu manyan shuwagabannin Boko Haram.

 

Sanarwar tace an samu Rahoton cewa Boko Haram na amfani da wani gida inda take baiwa mayakanta horo a ciki kuma akwai wasu manyan shuwagabannin kungiyar a ciki.

 

Da samun wannan labari ne sai Hukumar sojin sama ta tashi jirage zuwa wadannan gurare inda ta yi ruwan bama-bamai akansu kuma ta kashe da dama daga cikin shuwagabannin kungiyar.

 

Karanta wannan  Sanata Ndume yace rayuwa a Maiduguri tafi kwanciyar hankali akan Abuja saboda matsalar tsaro

Kalli bidiyon a kasa:

Sabuwar Rundunar Operation Long Reach dake karkashin rundunar Operation Lafiya Dole ce ta kai wannan samame.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.