Matar gwamnan Benue, Eunice Ortom ta kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 inda tace ita da danta sa wasu ma’aikatanta duk sun kamu.
A sanarwar data fitar Ranar Jum’a ta bayyana cewa NCDC ta aika musu sakamakon gwajin da aka musu a gidan gwamnati.
Tace daga yanzu ita da dan nata da sauran ma’aikatan nata zasu shiga killacewa kamar tanda dokar NCDC take.
Ta yi kira ga mutane dasu kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar. Inda tace idan ta kama mutum ba wai shikenan mutuwa zai yi ba.