Kungiyar SERAP dake kula da kae hakkin bil’adama ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari daya gaggauta janye yafiyar daya yiwa tsaffin gwamnonin Plateau da Taraba, Joshua Dariye da Rev. Jolly Niame.
A ranar alhamis ne shugaba Buhari ya yafewa mutane masu laifi dake gidan yari guda 159 laifukansu wanda a cikin hadda wa’yan nan gwamnonin.
Amma kungiyar dake kula da kare hakkin bil’adama ta bukaci shugaba Buhari ya janye yafiyar tasa akansu, domin bai kamata a riga yafewa barayi kamarsu laifuka ba don wasu ma zasu iya aikata irin laifin.
Dariye da Niame sun kasance a gidan yari tun bayar saukar su a mulki bayan da kowannen su ya saci kudi na naira biliyan 1.16.