fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Da Dumi Dumi:Messi ya gayawa Neymar cewa yana so ya koma kungiyar Paris Saint German

Kungiyar Paris Saint German ta kara samun gwarin gwiwa wurin siyan mashahurin dan wasan tamola na kungiyar Barcelona, wato Lionel Messi wanda kwantirakin shi zai kare a karshen wannan kakar.

Watanni shida ne kacal suka rage a kwantirakin Messi na Barcelona yayin da yanzu ya samu damar fara tattaunawa da wasu kungoyin dake harin siyan shi.

Har yanzu dai kungiyar Manchester City wadda tayi yunkurin siyan dan wasan a kakar bara tana jin cewa itace zata yi nasarar siya messi a karshen wannan kakar, amma labari ya canja bayan da wani dan jaridar kasar Brazil ya bayyana Messi ya gayawa Neymar cewa yana so ya koma PSG.

Karanta wannan  Manchester United zata dauki Casemiro daga Real Madrid

Dan jaridar daya watsa wannan labarin ba kowa bane illa Thaigo Asmar wanda ya kara da cewa Messi da tsohon abokin aikin nashi suna tattaunawa ne a kafar sada zumunta ta Whats App, inda Messi ya bayyanawa Neymar ra’ayin shi na komawa kungiyar zakarun Faransan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.