Kungiyar Malaman jami’o’i ta kasa, ASUU ta daukaka kara baya kotu tace mata ta gaggauta janye yajin aiki ta koma makaranta.
Shugaban kungiyar ASUU Emmanuel Osodoke dama ya bayyana cewa zasu tattauna akan wannan shari’ar da aka yi ranar laraba.
Yayin da aka samu labari yau ranar juma’a cewa kungiyar malaman ta daukaka kara domin bata gamsu da wannan shari’ar da aka yi ba.
Gwamnatin tarayya ce ta maka ASUU a kotu kan wannan yajin aikin data ke yi har na tsawon watanni bakwai, wanda hakan yasa yara ke zaune a gida basa zuwa makaranta.