fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Da Dumi Duminsa: Babban Bishop na Cocin Omega Ministry (OPM), Apostle Chibuzor Chinyere dake Fatakwal ya yi tayin mayar da iyayen marigayiya Deborah Samuel zuwa Fatakwal

Da Dumi Duminsa: Babban Bishop na Cocin Omega Ministry (OPM), Apostle Chibuzor Chinyere dake Fatakwal ya yi tayin mayar da iyayen marigayiya Deborah Samuel zuwa Fatakwal.

Fassara Global Access Hausa

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ‘ dalibai Yan’uwanta ne suka kashe marigayiya Deborah Samuel ‘yar aji biyu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato a ranar Juma’a, biyo bayan zargin ta da zagin Manzon Allah (SAW) a ranar Alhamis.

Labarin kashe budurwar ya zama abin damuwa da kuma tattaunawa ga ‘yan Najeriya wanda sun bukaci a gudanar da bincike mai zurfi kan kafin faruwar lamarin da kuma lokacin da lamarin ya faru.

Bayan faruwar lamarin, mahaifiyar Deborah, Alheri Emmanuel ta sha alwashin cewa ba za ta sake barin daya daga cikin ‘ya’yanta bakwai da suka rage ya tafi makaranta ba domin gujewa fadawa irin abinda ya faru da ‘yarta na alkawari.

Mijin kuma mahaifin Deborah da aka kashe, Mista Emmanuel Garba, ya bayyana cewa a matsayinsa na Kirista nagari, shi da iyalinsa sun yanke shawarar cewa ba za su je kotu ba a kan rashin ‘yarsu amma sun bar kome wa Allah.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya ta bayyana farashin da za'a sayar da litar mai tace zata hukunta gidajen man dake sayar da litar fetur naira 180

Da yake mayar da martani kan hakan, Apostle Chibuzor na Cocin Omega Power Ministries (OPM) ya shiga dandalinshi na sada zumunta inda ya roki wadanda sun san iyayen Deborah su gaya musu da su tuntube shi da wuri-wuri, inda ya yi alkawarin mayar da daukacin iyalin garin Fatakwal domin cigaba da rayuwa..

Ya rubuta “Na kalli faifan bidiyo inda iyayen Deborah Samuel suka ce ba za su sake tura yara zuwa makaranta ba. ALLAH YA KIYAYE.

“Duk wanda ke da alaka dasu ko ya wayesu to ya sanar da su nan take cewa ni Apostle Chibuzor Chinyere babban Bishop na Cocin OPM a Fatakwal yana so ya kawosu nan Fatakwal.

“Za su kasance a ɗaya daga cikin rukunin gidaje kyauta na Omega Power Ministries (OPM) ba za su taɓa biyan haya ba har abada. Duk yaran da suke dashi zasuyi Karatu a makarantinmu na OPM zan basu tallafin Karatu har jamiya.

Mai Karatu me zaka ce?

Jaridar Vanguard

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.