Babbar kotun jihar Kano dake Audu Bako ta yankewa wanda ya kashe Hanifa, Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta rataya.
Yayin da shima abokin aikin nasa daya taya shi garkuwa da yarinyar yar shekara biyar, Isayaku Hashim shima za a kashe shi ta rataya.
Sai kuma matar da suka aikata aikin tare da ita, Fatima Jibril itama aka yanke mata bukucin shekaru biyu a gidan Kurkuku.
Tanko ya kasance malamin dake koyar da Hanifa a makaranta, amma kuma duk da haka yayi garkuwa da yarinyar ya aikata barzahu.