Shugaban dakarun sojin Najeriya, Lucky Irabor ya kalubalanci gwamna Matawallen Zamfara bisa maganar da yayi na cewa a baiwa talakawa lasisin mallakar bindigu don kare kanwunansu.
Inda yace gwamnan bashi da wannan ikon na umurtar kwamishinan ‘yan sanda cewa yaba talakawa lasisin mallakar bindigu don yakar ‘yan bindiga.
Inda yace hakkain hukuma ne ta yaki ‘yan bindiga ba mutanem gari ba, kuma bai san inda gwamnan ya samu wannan ikon ba, amma za’a tambaya lauya aji ko yanada wannan ikon.