Kungiyar Barce ta taya dan wasan gaba na kungiyar Bayern Munich da take harin saya dan shekara 35 watau, Robert lewandowski.
Bayern Munich ta sakawa tauraron nata farashin yuro miliyan 34 ne, kuma manema labarai na AS a kasar sifaniya sun bayyana cewa Munich zata maye gurbinsa da Ronaldo.
Cristiano Ronaldo na shirin barin Manchester United bayan da kungiyar taki sayen sabbin ‘yan wasa kuma da yiyuwar ya koma Bayern Munich ta gasar Bundesliga.