Tauraron dan wasan Liverpool na gaba, Sadio Mane na daf da barin kungiyar ya koma kungiyar zakarun gasar Bundesliga, Bayern Munich.
Kuma yanzu gwanin kasuwar kwallon kafa Fabrizio Romano ya bayyana cewa Munich ta yiwa dan wasan tayin kwantirakin shekaru uku kuma ya amince.
Abinda ya rage yanzu shine ta kammala sayensa bayan Liverpool tayi watsi da tayi biyu datawa dan wasan, amma ana sa ran Munich zata taya shi a farashin mai kyau bada dadewa ba.