fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Da Dumi Duminsa: Bola Tinubu ya zabi Masari a matsayin abokin takararsa

Yayin da ‘yan takarar shugaban kasa ke kokarin bayyana abokan takararsu kafin wa’adin da hukumar zabe ta INEC tasa masu ya cika,

Dan takarar jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya zabi dan jihar shugaban kasa, watau Kabir Ibrahim masari wanda ya kasance amintacce a Katsina.

Bola Ahmad Tinubu ya zabe shi amma da yiyuwar a canja shi domin dole sai masu hannu da tsaki a jam’iyyar sun amince da shi kafin a tabbatar dashi a matsayin abokin takarar nasa.

Kuma Tinubu zai gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yau akan wannan maganar inda yace har yanzu suna cigaba da fafutukar neman abokin takarar nasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.