fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Da Dumi Duminsa: Cristiano Ronaldo yace zai sake bugawa kasarsa wata asar bayan kofin duniya na wannan shekarar

Tauraron dan wasan gaba na kungiyar Manchester United, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa gasar kofin duniya da za a buga wannan shekarar a kasar Qatar ba itace gasa ta karshe da zai bugawa kasar Portugal ba.

Inda ya kara da cewa yana da burin bugawa kasar tasa gasar Euro ta shekarar 2024 bayan gasar kofin a kasar Qatar.

Cristiano Ronaldo baya jin kasancewarsa a Manchester United domin baya samun damar buga wasanni a wannan kakar sosai wanda hakan yasa kwallo guda kacal yaci mata.

Kuma hakan ya biyo baya ne bayan ya bukaci a sayar da shi amma babu kungiyar data neme sa a kasuwar data gabata.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.