Hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa da yiyuwar ta damke shugaban sanatoci Ahmad Lawal, da tsohon gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio da dai sauran su.
Dalili shine sun nemi takarar kuje fiye da daya a lokaci guda wanda hakan ya sabawa dokar INEC ta shekarar 2022.
Ma’aikcin INEC na jihar Akwa Ibom, Mike Igni ne ya bayyana hakan yayin dayake ganawa da manema labarai na Channels TV ranar talata.
Inda yace gabadayansu sun nemi kujera sama da daya a lokaci guda kuma hakan ya sabawa dokar hukumar zabe ta shekarar 2022,
Sannan hukuncin su shine shekaru biyu a gidan yari tare da sauran mutanen da suka aikata irin wannan laifin a wannan laifin.