Bayan kammala zaben fidda gwani na gwamnonin jam’iyyar APC, daya daga cikin manyan ‘yan takarar APC dake neman gwamna a jihar Taraba ya fice daga jam’iyyar,
Watau farfesa Muhammed Sani Yahaya, inda ya bayyanawa manema labarai ra’ayin nasa a babban birnin jihar, Jalingo.
Mohammed tare da wasu membobin APC duk sun bayyana cewa zaben ba’a yi shi a bisa adalci saboda haka ne ya fice daga jam’iyyar.
Kuma har yanzu bai kammala yanke shawara akan jam’iyyar da zai koma ba.