Tuesday, November 11
Shadow

DA DUMI DUMINSA: fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Sama da mutanen Arewa kimanin Miliyan 60 Suka Nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027, al’ummar Arewa sama da Miliyan 60 Sun Bayyana Goyan bayan Su ga Tinubu

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Sama da mutanen Arewa kimanin Miliyan 60 Suka Nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027, al’ummar Arewa sama da Miliyan 60 Sun Bayyana Goyan bayan Su ga Tinubu.

Fadar shugaban ƙasa tace Sama da Mutanen Arewa Miliyan 60 Sun nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu, da Wasu da Kungiyoyi ga tuntuba ta matasan Arewa ta wakilta, sun bayyana Goyon bayansu ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Sun jaddada cewa “goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Sanata Akpabio suna mai cewa “shugabannin biyu daga Kudu sun goyi bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban ƙasa da Shugaban majalisar Dattawa, kuma hakan ya dace a gare mu. don rama wannan gudummawar da suka bamu.”

Karanta Wannan  Dokar-ta-ɓaci: Magoya bayan Fubara na gudanar da gangamin maida shi kan kujerarsa

Al’ummar Arewa, Sun ya yabawa shugaba Tinubu kan nasarorin da ya samu ta fuskar bunkasa karfin dan Adam da ababen more rayuwa. Ya bayyana wasu tsare-tsare irin su babban titin bakin teku, hukumar raya Kudu maso Gabas, Asusun NYSC Trust Fund, da kuma tsarin lamuni na dalibai a matsayin shaida na jagoranci na gaba na Tinubu a karkashin shirin Renewed Hope. Yusuf ya yarda cewa, duk da kalubalen tattalin arziki, Gwamnatin Tinubu ta tafiyar da harkokin kasar yadda ya kamata ba tare da tara basussuka da ya wuce kima ba.

Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa ta yi kira da a baiwa gwamnati hakuri da kuma hadin kai a yayin da ake ci gaba da kokarin gina Najeriya mai inganci.

Karanta Wannan  Na Gano cewa: Yawanci mazan Kano basa iya ciyar da matansu, sannan ana yiwa yara mata auren wuri>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *