fbpx
Monday, August 15
Shadow

Da Dumi Duminsa: Firaym Ministan kasar Landan yayi murabus

Firaym Ministan kasar Landan, Boris Johnson dan shekara 58 yayi murabus bayan shekaru uku yana mulki.

Johnson ya bayyana hakan ne yau ranar alhamis inda yace yana bakin sanar da mutane cewa yayi murabus a matsayinsa na firaym mimistan kasar Landan.

Ya kara da cewa yana godiya ga dumbin mutanen da suka mara masa baya ya zamo ministan kasar a shekarar 2019, kuma zai cigaba da zama a ofishin har dai an zabi sabo.

Johnson yayi murabus ne bayan munistocin kasar da dama sunyi murabus da kuma zanga zangan kan cewa sai ya bar kujerar tasa, kuma yace yana bakin cikin hakan domin wannan shine aiki mafi girma a fadin duniya bakidaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.