fbpx
Friday, July 1
Shadow

Da Dumi Duminsa: Gwamna Rotimi Akeredolu ya gargadi APC akan tsayar da dan arewa a matsayin dan takararta na shugaban kasa

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya gargadi jam’iyyar APC akan tsayar da dan arewa a matsayij dan takarar shugaban kasa na zaben shekarar 2023.

Inda yace dan kudu ya kamata jam’iyyar ta tsayar idan har tanaso ta cigaba da mulkin kasa Najeriya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan da jam’iyyar ta bayyana cewa shine zai jagoranci taron zabenta na fidda gwani a ranar 6 ga watan yuni.

Amma mutane da dama na tunanin cewa APC dan arewa zata tsayar saboda PDP ta tsayar da Atiku Abubakar, kuma shugaban sanatoci Ahmad Lawal na daya daga cikin manyan ‘yan takarar da zata iya tsayarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.