Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike na ganawa da gwamnonin PDP da suka mara masa baya a lokacin daya tsaya neman tikitin takarar shugaban kasa na PDP.
Sun fara gudanar da wannan gagarumin taron ne awa guda data gabata a gidan gwamonin nasu dake babban birnin tarayya Abuja.
Kuma duk da cewa dai a sirrince suke gudanar da taron, ba zai wuce kan shawo kansa ya fasa sauya sheka ba saboda matsalar daya samu da Atiku Abubakar.
Atiku ya doke Wike a zaben fidda gwani kuma bayan wannan an nemi ya gwamnan Rivesr din a matsayin mataimakinsa amma yaki, wanda hakan yasa gwamnan ya kullace shi a rai tun watan Mayu.