fbpx
Monday, June 27
Shadow

Da Dumi Duminsa: Gwamnonin APC sun aikawa Buhari sunayen ‘yan takarar shugaban kasa daga kudu guda biyar ya zabi daya a ciki

Gwamnonin jam’iyyar APC sun kaiwa shugaba Buhari sunayen ‘yan takara biyar dake neman shugabancin Najeriya ya zabi daya a cikinsu, Daily Trust suka ruwaito.

Rahoton ya kara da cewa gwamnonin bayan ganawa da shugaban kasar ne suka aika masa da sunayen guda biyar da safiyan ranar talata, 7 ga watan yuni.

Wanda suka hada da mataimakinsa farfesa Yemi Osinbajo, tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, gwamnan Ekiti Fayemi Kayode, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi da kuma gwamnan Ebonyi, David Umahi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.