fbpx
Monday, August 15
Shadow

Da Dumi Duminsa: Gwmamna Uzodimma ya gargadi ‘yan bingar jihar Imo su bar jihar nan da kwanaki goma kafin zuwan shugaba Buhari

Gwamnan jihar Imo, Uzodimma ya shawarci ‘yan bindiga cewa su mika wuya su bayar da makamansu nan da kwanaki goma.

Domin yace ce a jihar Imo za’a gudanar da taron shekara na dakarun sojin Najeriya daga ranar 30 ga watan yuni zuwa ranar 6 ga watan Yuli.

Kuma yace za’a zuba dakarun tsaro sama da 10,000 a jihar wanda suka hada da sojojin sama dana kasa dana ruwa dama hukumar ‘yan sanda bakidaya.

Kuma yace shima shugaba Buhari ranar 12 ga watan Yuli zai ziyarci jihar domjn bayar da kamashon tituna a jihar.

Karanta wannan  Labari me dadi: 'Yan bindiga sun sako mutane 35 da sukayi garkuwa dasu a Millennium City dake jihar Kaduna

Saboda haka yana shawartarsu dasu mika wuya domin zasu yi amfani da wannan damar wurin yakar gabadaya ‘yan ta’addan dake boye a cikin dajin jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.