Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta tabbatar da barkewar cutar Monkeypox a fadin duniya.
Tedros Ghebreyesus shugaban hukumar ne ya bayyana hakan a yau ranar asabar, biyo bayan barkewar annobar a kasashen duniya.
Inda yace akwai wasu kasashen da basu tabbatar da barkewar cutar ba amma duk da haka shi ya tabbatar da ita domin ta fara mamaye duniya.
Wannan cutar itace ta farko da hukumar kiwon lafiyar ta tabbatar da barkewarta a fadin duniya bayan Covid-19.