Hukumar ‘yan sandan jihar Legas ta danke shararren mawakin Najeriya, Ice Prince Zamani da laifin yin garkuwa da wani jami’inta.
Mai magana da yawun hukumar na jihar ne ya bayyaba hakan, Benjamin Hudeyin inda yace Ice Prince na tuka mota babu lamba ne da safiyar ranar juma’a yayin da lamarin ya faru.
Ya kara da cewa dan sandan ya tsayar dashi ne domin tantance waye a cikin motar da ake ukawa babu lamba, amma sai yayi garkuwada jami’in bayan ya shiga motar kuma yayi masa barazana.
A karshe yace zasu cigaba da rikonshi a ofoshinsu kafin su maka shi a kotu anjima kadan.