Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta bayyana cewa ba zata bari a canja abokan takara ba kamar yadda jam’iyyun siyasa keyi, inda suke bayyana sunan wasu kafin su samo na asalin da suke so su saka.
Hukumar zaben ta bayyana cewa ranar 17 ga watan yuni ce wa’adin data sakawa ‘yan takarar shugaban kasa su bayyana mata abokan takararsu, inda wasu ‘yan takarar kamar Tinubu da Peter Obi sukace suka bata sunayen wasu amma zasu canjasu nan gaba.
Sai dai kwamishinan hukumar Zaben Barrister Festus ya bayyana cewa ba zasu lamince wannan maganar tasu ba domin babu hakan a kundin tsarin mulkin Najeriya.