fbpx
Monday, August 15
Shadow

Da Dumi Duminsa: INEC ta bayyana sunayen ‘yan takarar sanatoci amma ta cire Ahmad Lawal da Godswill Akpabio

Hukumar zabe ta INEC ta cire sunan shugaban sanatoci Ahmad Lawal da tsohon ministan jihar Niger Godswill Akpabio yayin data bayyana sunayen ‘yan takara na jam’iyyu 18 dake Najeriya ranar juma’a.

Ahmad Lawal da Godswill Akpabio basuyi zaben fidda gwani ba na sanata amma duk da haka saida APC ta mikawa INEC sunayen su a matsayin sanatocinta na arewacin yobe da kuma arewa masu yammacin Delta.

Hukumar INEC din ta maye sunayensu ne dana Bashir Machina and Udom Ekpoudom, wanda su ma dai jam’iyyar ta APC bata mikawa INEC sunayensu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.