fbpx
Sunday, August 14
Shadow

Da Dumi Duminsa: Kasar Amurka ta hallaka shugaban ‘yan ta’addan Al Qaeda, Ayman Al Zawahiri

Dakarun sojin sama na kasar Amurka sun hallaka kasurgumin dan ta’addan daya addabi duniya, wato Ayman Al Zawahiri.

Ayman Al Zawahiri ya kasance shugaban ‘yan ta’addan Al Qaeda kuma ya jagoranci kai hare da hare da dama sannan an dauki tsawon shekaru sama da 20 ana nemansa.

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ne ya bayyana hakan a ranar litinin yayin dayake yin jawabi a fadarsa ta gidan White House.

Inda yace ita dama Amurka bata barin duk wani mahalukin daya takurawa al’ummarta a raye face ta aika shi barzahu.

Karanta wannan  Naira miliyan 650 masu garkuwa da mutane suka samu a cikin shekara guda-Bincike

Saboda haka yana mai farin sanar da duniya cewa jajirtattun dakarun sojojin sama na kasarsa sun hallaka gagarabadau, wato Ayman Al Zawahiri shugaban ‘yan ta’addan Al Qaeda.

Ya kara da cewa sun kashe shine a kasar Afghanistan kuma basu jiwa kowa rauni ba face shi kadai hatta iyalansa basu taba ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.