fbpx
Friday, March 31
Shadow

Da Dumi Duminsa: Kotu bata wanke Nnamdi Kanu ba sallamar shi kadai tayi, cewar ministan shari’a

Ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa kotun daukaka kara ta tarayya bata wanke shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB ba, wato Nnamdi Mazi Kanu.

Inda yace sallamar shi kadai tayi, saboda haka yanaso al’umma su fahimci cewa kotu bata wanke shi gabadaya ba akwai sauran tambaya akansa.

Yace laifukan da ake zarginsa da aikatawa har yanzu dai suna nan akansa kuma zai amsa tambayoyi gami dasu.

A jiya ranar alhamis ne kotun daukaka kara ta sallame Nnamdi Kanu inda lauyansa ya bayyaba cewa an wanke shi amma yanzu gwamnatin tarayya tace bata wanke shi ba.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *