Kingiayar ma’aaikatar matuka jiragen sama ta Najeriya, ANAP ta gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya gaggauta biyawa ASUU bukatunsu yara su koma makaranta.
Hakan ya biyo baya ne bayan kungiyar ‘yan Kwadago ta NLC ta bayyana cewa a mako mai zuwa ranar talata zata gudanar da zanga zanga a fadin kasar kan yajin aikin ASUU.
Yayin ita ita ma kungiyar NUBIFIE ta ma’aikatan bankuna da kuma inshora tace itama zata shuga ayi zanga zangar da ita.
Kungiyar malamai ta ASUU ta dauki tsawon watanni biyar tana yajin aiki biyo bayan gwamnatin Najeriya taki cika alkawarin data yi mata.
Kuma tattalin arzigin kasa Najeriya zai matukar girgiza idan har kungiyar ma’aikatar jiragen sama ta daina yin aiki kamar yadda ta fadi zata yi idan ba’a biyawa ASUU bukatunsu ba.