Kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasaha ta Polytechnic dake jihar Delta ta baiwa gwamna Okowa gargadi na kwanaki talatin cewa zata tafi yajin aiki.
Ta bashi wannan gargadin ne biyo bayan sabon tsarin daya kawo masu na cewa suna zasu hada kashi goma na albashin su yayin da kuma gwamnati zataji da sauran.
Wanda hakam yasa kwalajin ta koka kan wannan lamarin tace matsin yayi yawa sosai domin basu samun albashi akan lokaci sannan kuma dalibai basa samun ingantaccen ilimi.
Tace hatta malaman da sukayi murabus da kuma wasu data kora ta kasa maye gurbinsu domin babu halin yin hakan, saboda haka taba gwamna Okowa kwanaki 30 ya janye wannan tsarin nasa.