fbpx
Monday, August 15
Shadow

Da Dumi Duminsa: Lionel Mesai zai fice daga Paris Saint Germain

Kungiyar Paris Saint Germain na shirin sayar da Lionel Messi a wannan kakar, cewar dan jaridar kasar Sifaniya, Pedro Morata.

Messi ya koma PSG ne a kakar bara daga Barcelona amma sai dai tauraruwarsa bata haskaka a gasar ta Ligue one ba, inda yaci kwallaye 11 kacal a wasanni 34 daya bugawa PSG.

Kuma dan wasan daya lashe kyautar Ballon D’or bakwai ya nuna kwazonsa a kwanakin nan inda ya taimakawa kasarsa ta Argentina ta lashe kofin Finalissima.

Kuma yaci kwallaye da dama, yayin shi kuma darektan PSG, Luis Campus yake shirin sayar da shi don yanaso ya gina tawagar kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.