fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Da Dumi Duminsa: Masu sayar da Burodi sun fara yajin aikin gargadi ga gwamnatin tarayya

Kamfanin dake sayar da Burodi na Premium sun fara yajin aikin gargadi ga gwamnagin tarayya na tsawon kwanaki hudu.

Inda mai magana da yawun kamfamin Mr. Thomas ya bayyana cewa sun fara yajin aikin ne saboda tsadar kayayyakin aikin da ake kera buredin da kuma kudin man Diesel.

Sannan ya kara da cewa kamfanin nasu na tafka asara sanadiyyar tsadar da kayayyakin kera buredin sukayi, kuma zasu cigaba da yajin aikik idan gwamnati bata yi wani abu akai ba.

A karshe yace buredi abinci ne mai matukar inganci kuma shi na kowa ne da masu kudi da talakawa kowa na cinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.