Masoyan kungiyar Real Madrid sun nemi shugaban kungiyar, wato Florentino Perez daya sayo tsohon dan wasanta wato Ronaldo.
Sun bayyana masa hakan ne yayin daya halacci filin atisayin kungiyar gabanin wasan su na sada zumunta da Barcelona ranar asabar.
Shugaban kungiyar bai basu amsa ba haka nan ya wuce, kuma masoyan sun ce masa kar ya bari Ronaldo ya koma Atletico Madrid domin tana neman shi.