fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Da Dumi Duminsa: Rundunar soji ta damke ‘yan bindigar da suka kashe mutane 40 a cocin katolika ta jihar Ondo

Rundunar sojin Najeriya tace ta damke ‘yan bindigar da suka kai hari cocin katolika ta Owo dake jihar Ondo suka kashe masu bauta.

A ranar biyar ga watan Yuni ne ‘yan bindigar suka kai wannan mummunan harin cocin, suka kashe mutane 40 kuma suka jigata wasu da dama.

Wanda hakan yasa har wasu al’umma ke yiwa ranar lakabi da bakar lahadi kan wannan mummuman harin da aka kaiwa masu bauta a cocin.

Amma shugaban rundunar sojin Najeriya, janar Lucky Irabor yanzu yace sun kama ‘yan bindigar da suka kai wannan harin.

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Yan bindiga sun kashe sojoji da 'yan sanda marasa adadi a jihar Enugu

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.