fbpx
Monday, August 15
Shadow

Da Dumi Duminsa: Shima abokin takarar Tinubu, Masari ya bayyana cewa ya batar da takkadun shaidar kammala makarantarsa

Abokin takarar me neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Kabiru Masari ya bayyana cewa shima ya batar da takaddun makarantarsa.

Manema labarai na Peoples Gazette ne suka wallafa wannan labarin inda sukace yace takaddun shadar kammala makarantar firamarinsa da sakandiri sun bata a shekarar 2021.

Saboda haka shima affidavit ya baiwa hukumar zabe ta INEC kamar yadda uban gidansa yayi, watau Bola Ahmad Tinubu.

Kuma hakan ya kara tabbatar da cewa Tinubu ya zabe shine na wucin gadi saboda kar ya sabawa dokar hukumar zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published.