fbpx
Monday, August 15
Shadow

Da Dumi Duminsa: Shuwagabannin APC guda uku sun sauya sheka kan zabar musulmi da musulmi da jam’iyyar tayi a matsayin ‘yan takararta na shugaban kasa

Membobin jam’iyyar APC na cigaba da sauya sheka daga APC bayan dan takarar shugaban Kasarta, Ahmad Tinibu ya zabi Musulmi a matsayin abokin takararsa.

Shugaban jam’iyyar na jihar Rivers Prince Tonye Wilson ne ya zamo shugaba na uku daya bar jam’iyyar bayan Dr. Dwari George da Ibim Semintinari.

Kuma dukkan su sun sauya shekar ne kan manufa guda watau domin jam’iyyar ta zabi Musulmi da Musulmi a matsayin ‘yan takararta na shugaban kasa.

A ranar laraba ne dn takarar shugaban kasar nata Bola Ahmad Tinubu ya zabi Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zabe mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.