Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad ya tafi jihar Katsina don bayyanawa shugaba Muhammadu Buhari abokin takararsa daya zaba.
A baya mun kawo rahoto na cewa Tinubu da Masari na Daura suna ganawa da Buhari a sirrince.
Amma yanzu an samu labari daga majiya mai karfi cewa Tinubu yaje Daura ne bayyanawa shugaban kasar Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.
Rahoton ya kara da cewa gwamna jihar Borno, Zulum ne ya roki Tinubu ya zabe mai gidansa Shettima akan ya zabe shi a matsayin abokin takararsa na zaben shekarar 2023.