‘Yan bindiga sun kaiwa jami’ar tsohon dan takarar gwamnan Rivers, Arthur Javis hari a dadren jiya ranar talata sunyi garkuwa da dalibi guda.
‘Yan bindigar sun bude masu wuta ne yayin da suke dawowa daga ajujuwansu suna kokarin zuwa makwancinsu a farfajiyar makarantar.
Inda wasu daga cikin daliban sukayi nasarar tserewa da raunika amma duk da haka saida suka kama guda daya a ciki su suka tafi dashi.
Kuma hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar wannan lamarin sannan tace ta bayar da umurni a bincike dalilin daya sa suka kaiwa jami’ar wannan hari.