‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane sama da hamsin a babbar motor haya da wasu kananun motoci kan hanyar Sokoto zuwa Gusau ranar asabar.
Mutanen suna hanyar dawowa ne daga biki a jihar Sokoto kamar yadda manema labarai na Premium Times suka ruwaito, inda ‘yan bindigar suka tare su a hanyar.
Daya daga cikin fasinjojin motar daya tsira, Lawal Ja’o ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a Dogon Awo karamar hukumar Tureta.
Inda yace sun sun tsere daji ne yayin da lamarin ke fauwa kuma ‘yan bindigar sunyi garkuwa da mutan sama da hamsin.