Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbaji zai shilla kasar Kwadebuwa yau ranar litinin, bayan ya fadi zabwn fidda gwani na shugaban kasa da APC ta gudanar.
Osinbajo zai je Abdijan ne don hakattar taron wata kungiyar ta Africa CEO wanda ake gudanarwa a kowace shekara.
An kafa kungiyar ne don cigaban Afrika kuma kungiyar na tare dasu Bankin Duniya da sauran manyan ma’aikatun duniya dake talkafa mata.
Yayin da zasu tattauna akan tattalin arzikin nahiyar bakidaya, kuma shuwagabannin Afrika da dama zasu halacci taron tare da wasu manyan ‘yan siyasa.