fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Da Dumi Duminsa:Gwamnatin jihar Zamfara tace kowa ya kowa ya sayi bindiga ya rika kare kansa don ta gaji da matsalar tsaro

Gwamnatin jihar Zamfara tace ba zata cigaba da lamintar hare-haren da ‘yan bindiga ke kai masu ba da kuma masu garkuwa da mutane.

Saboda haka ta umurci kwamishinan ‘yan sanda daya baiwa mutanen da suka cancanta lasisi na yin amfani da bindiga don kare kansu.

Inda gwamnatin ta kara da cewa zata baiwa masarautun jihar guda 19 fom din lasisin bingidar guda 500 don ta baiwa mabukata da suka cancanta.

A karshe gwamnatin tace musamman manoma ya kamata su samu bindugun don su rika kare kawunansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.