fbpx
Friday, July 1
Shadow

Da Dumi Duminsa:Kotu ta saka ranar da zata saurari karan da aka shigar kan Atiku na cewa shi ba asalin dan Najeriya bane

Babbar kotun tarayya ta Abuja tace zata saurari karan da aka shigar mata akan  Atiku ranar 20 ga watan Yuli, na cewa shi ba dan asalin kasar Najeriya bane.

A watan mayu ne tsohon mataimakin shugban kasa, Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Amma yanzu lauya Johnmary Jideobi ya shigar da karan akan Atiku cewa bai cancanci ya nemi takarar shugbancin Najeriya ba domin shi ba cikakken dan kasar bane.

Kuma dama a shekarar 2019 lokacin daya nemi wannan kujerar an shigar  kara makamancin wannan akasa amma kotu tayi watsi dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.