fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Da Dumi Duminsa:”Shugaba Buhari bai ce a baiwa dan kudu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa ba”>>Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin dake bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari yace a baiwa dan kudu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a APC.

Wannan labarin ya biyo bayan ne bayan da kunguyar matasan Arewa ta AYCF ta kalubalanci wasu gwamnonin Arewa da suke goyon bayan baiwa ‘yan kudu tikitin takarar shugaban kasa.

Inda hadimin Buhari, Garba Shehu ya bayyanawa BBC cewa shugaba bai tattauna akan baiwa ‘yan kudu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a APC ba,

Ya shawarci masu neman kujerar ne dasu gudanar da zaben fidda gwani cikin limana kuma tsayar da dan takarar da zai sa jam’iyyar tayi nasara.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *