fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Da Dumi Dumisa:Hukumar NDLEA ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 679 a jihar Jigawa ta kwace kwaya mai nauyin kilo 325.6

Hukumar dake yaki akan safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayyana cewa ta kama mutane 679 a jihar Jigawa kuma ta kwace kwaya mai nauyin kilo 325.6 daga watan yuni na shekarar 2021 zuwa yanzu.

Kwamandan hukumar na jihar Jigawa, Ibrahim Braji ne ya bayyana hakan game da zagayowar ranar hana ta’ammali da miyagun kwayoyi a 26 ga wannan watan.

Kuma yace cikin mutanen da suka kama hadda mata guda takwas A karshe dai yace taimakon sauran jami’an tsaro na taimaka masu sosai wurin kama masu ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.