fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Da Dumi-Dumi:’Yan Bindiga sun sace mutane 25 a daren jiya a Zamfara

Rahotannin dake fitowa daga jihar Zamfara na cewa ‘yan bindiga da suka shiga garin Bindin na karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara sun sace akalla mutane 25.

 

‘Yan bindigar sun tare hanyar shiga garin inda suka rika shuga gida-gida suna zakulo mutane. Bayan sun gama tarasu suka shiga daji dasu suka kuma bukaci ‘yan uwansu da su biya kudin fansa kamin a sakesu.

 

Wani mutum daya ya kubuta daga hannunsu yayin da suka saki wata mata saboda tana shayar da jaririnta.

Karanta wannan  Gwamna matawalle yace sojoji su fara bi gida-gida suna kashe 'yan bindiga a Zamfara, kuma duk wanda ya saba dokar hawa babur a harbe shi

 

Ba’a samu jin ta bakin kakakin ‘yan bindigar jihar,Muhammad Shehu ba a yayin hada wannan rahoto kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.