fbpx
Monday, December 5
Shadow

Da Duminsa: “A watan gobe za’a saki Nnamdi Kanu”

A yayin da kotu ta wanke shugaban Kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu daga laifuka 8 cikin 15 da ake zarginsa da aikatawa,  masoyansa sai murna suke.

 

Hakan yasa suke ta hango masa nasara a shari’ar da ake yi tsakaninsa da gwamnatin tarayya.

 

Ana zargin Nnamdi Kanu da aikata laifukan cin amanar kasa da kuma tunzura matasa su yi bore ko daukar makamai da sauran wasu zarge-zarge.

 

Babban fasto a cocin Awka dake jihar Anambra, Most Revd. Alexander Ibezim Ya bayyana cewa, ya hango za’a saki Nnamdi Kanu a watan da zamu shiga na Mayu.

Karanta wannan  Ɗalibin da yai suka ga Aisha Buhari ya bata hakuri bayan ta janye ƙarar da ta kai shi

 

Ya bayyana cewa a watan Mayu akwai farin ciki sosai dan za’a saki Nnamdi Kanu sannan kuma za’a samu saukin hare-haren da ake kaiwa yankinsu na Kudu maso gabas.

 

Ya bayyana cewa Allah zai taba zuciyar Shuwagabannin Najeriya ta sassauto ta yanda zasu Saki Nnamdi Kanu dan kashe-kashen da ake a yankinsu ya tsaya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *