fbpx
Saturday, February 27
Shadow

Da Duminsa: Akwai yiyuwar Gwamnati ta rage farashin Man fetur zuwa Naira 160 nan da watan Disamba

Matsin lambar da kungiyoyin fafutuka sukewa gwamnatin tarayya akan ta mayar da farashin man fetur zuwa Naira 160 na nuna Alamar nasara.

 

Bayan zaman tattaunawar da aka yi tsakanin Gwamnatin da kungiyoyin Kwadago,a daren jiya, Gwamnatin ta bayyana cewa zata je ta yi nazari akan wannan lamarin da Kuma tuntuba inda ake tsammanin zata dawo da sabon farashin a ranar zama ta gaba, watau 7 ga watan Disamba.

 

Ministan Kwagado, Chris Ngige ya bayar da tabbacin cewa, duk da yake cewa gwamnati ta tsame hannunta kan kayyade farashin Man fetur din amma zasu je su tattauna da shugaban kasa da kuma Minstan mai da kwararru a harkar tattalin arziki gane da lamarin.

“The message from the organised Labour is clear; they want a reversal of the pump price of PMS. The parties have agreed to let the government side consult their principal on that. We will consult the President, minister of Petroleum and the Economic Management Team.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *